'Yan Sanda Sun Kama ‘Yan Bindiga 15 a Jihar Katsina

Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta bayyana cewa ta cafke wasu ‘yan bindiga 15 tare da kwato shanu da tumaki 495.

Jami’an tsaro sun samu nasarar dakile ayyukan 'yan bindiga a yankunan kananan hukumomi 8 inda ayyukan maharan suka fi kamari a jihar Katsina har kuma suka kama wasu daga cikin mayakan da madugunsu.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, Gambo Isah, wanda ya tabbatar da kamen ya shaida wa Muryar Amurka cewa bisa ga wasu sahihan bayanan sirri da suka samu, shugaban 'yan sandan karamar hukumar Dutsinma ya jagoranci wata tawagar ‘yan sanda da ‘yan banga zuwa kauyen Tsaunin Bala a karamar hukumar Danmusa har suka sami nasarar cafke wasu mutane 11 da jagoransu, Alhaji Adamu wanda aka fi sani da "SHANTAL" kuma suka kwato dabbobi 185 da tumaki 54.

Yan Bindiga Barayin Shanu A Katsina

A gefe guda kuma, shugaban 'yan sandan karamar hukumar Batsari ya jagoranci sintirin da ake kira "Operation Puff Adder" da na Sharar Daji" da tawagar 'yan banga daga yankin Dankar zuwa kauyen Dangayya a karamar hukumar Batsari har suka cafke wasu mutane 3 da ake zargin 'yan fashin dabbobi ne aka kuma yi nasarar kwato shanu 43 da tumaki 213 da ake kyautata zaton na al'ummar yankin ne da aka sace.

Ga Sani Shuaibu Malumfashi da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Sanda Sun Kama ‘Yan Bindiga 15 a Jihar Katsina