Bayan da kura ta dan lafa dangane da ayyukan ta'asar da 'yan bindiga ke yi a yankin gabashin Sokoto, wasu sassa na jihar yanzu ne suke kokawa akan rashin tsaron.
Yankin karamar hukumar Shagari, wanda shi ma a can baya ya soma fuskantar ayyukan ta'addanci kafin daga baya su yi sauki, yanzu abin ya fara waiwayowa.
A karshen makon da ya gabata wasu 'yan bindiga sun kai hari a wani kauye da ake Kira Horo Birni.
Malam Usman Horo Mai jakkai, na daga cikin wadanda suka tsallake rijiya da baya a lokacin da maharan suka shiga kauyensu, ya ce sun shiga gidansa ya samu ya sha da kyar amma suka harbe matarsa har lahira.
Mutane a kananan hukumomin da ke yankin kudancin Sokoto sun tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun addabi yankin domin wani lokaci ma akan gansu akan babura suna kai da komo a cikin jeji, kamar yadda wani wanda bai so a ambaci sunansa ba ya shaida.
Kananan hukumomin da ke Arewacin Sokoto da suka hada da Gudu, Tangaza da Binji su ma suna cikin halin kunci domin kusan a duk rana ba za a rasa ayuykan ta'addanci ko satar mutane, ko kuma fashi da makami a yankin ba.
Jagororin al'ummomin yankunan dai na dada kara yin kira ga jama'a akan su hada kai da jami'an tsaro don ceto yankunan daga wadannan matsalolin.
Saurari karin bayani a sauti:
Facebook Forum