Rundunar ta ce wadannan mutane sun kware ne da fashi a inda ake ciran kudi da ake kira POS in da sukan bi wadannan wurare su kuma yi amfani da makamai su kwace kudaden wadannan mutane dake aikin POS.
Ta ce wasun su kuma kan je bankuna ne su dunga sa ido kan wadanda ke ciran kudi inda sukan bisu a baya su kuma san yadda za su saci kudin da mutanen suka karba.
Kwamishinan 'yan sandan jihar Bornon Bello Magashi ne ya bayyana haka ga manema labarai ind ya ce wadannan mutane suna gudanar da wadannan aika-aika ne a jihar Borno dama wasu jihohi da ke Arewacin Najeriya.
SP Edet Okonde shi ne kakakin rundunar 'yan sandan Jihar Bornon ya kuma yayi ma manema labarai jawabi a madadin kwamishinan 'yan sanda inda ya ce jami'an 'yan sandanmu sun kama su ne a biranen Maiduguri da jalingo dake jihar Taraba.
Sun kuma amsa cewa sun aikata wannan aika- aika a jihar Kano da garin Abuja da Sakkwato, Zamfara, Jigawa, Jos da Damaturu. Sannan kuma an kame wasu motoci guda biyar da suke aikata wannan aika- aika dasu.
Rundunar ta Kuma kame wasu mutane guda biyar da suka balle wata mota a sakatariyar Musa Usman dake cikin garin Maiduguri, inda suka kwashe Naira miliyan 23.
Muryar Amurka ta kuma samu daman yin magana da wadannan mutane da ake zargi, wanda akasarin su, sun amsa laifuffukan.
Rundunar tace zata gurfanar da dukkanin wadannan mutane a gaban kuliya da zaran ta kammala bincike akan su.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5