'Yan Sanda Sun Kama Ice Prince Zamani A Legas

Ice Prince

Mawaki Ice Prince ya shiga hannun jami'an tsaro da sanyin safiyar yau Jumma'a a jihar Legas akan yin tuki da lambar mota mara lasisi, da kuma yi wa jami'in dan sanda barazana.

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama Shahararren mawakin nan na Najeriya Panshak Henry Zamani da aka fi sani da Ice Prince, bisa laifin yin garkuwa da wani jami’in dan sanda da kuma yi masa barazana.

A wani sakon twitter, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da kamen a yau Jumma’a kuma a yau din za a gurfanar da shi gaban kuliya a cewarsa.

A cewar Hundeyin, da misalin karfe 3 na safiyar Juma'a, aka tsayar da Ice Prince saboda yana tuki da lambar mota mara lasisi, ya kuma amince a kai shi ofishin ‘yan sanda.

Kakakin rundunar 'yan sandan ya ce daga baya sai ya yi garkuwa da dan sandan da ya tafi da shi a cikin motarsa, ya ci zarafinsa tare da barazanar jefa shi a cikin kogi.