'Yan Sanda Sun Kama Gungun Rikakkun ‘Yan Fashi Da Makami A Katsina

  • VOA Hausa

'Yan sanda Najeriya yayin wani atisaye da suka yi a Abuja (Hoto: Facebook/Rundunar 'Yan sandan Najeriya - Wannan tsohon hoto ne)

Wadanda aka kaman sun hada da, wani gungun batagari mai mambobi 7 da ake zargin ‘yan fashi da makamin da suka tare matafiyan dake safarar atamfofi da yaduddukan da aka kiyasta kudinsu zai kai Naira miliyan 4.

Rundunar ‘yan sandan Katsina ta kama akalla batagari 15 da take zargi da aikata laifuffuka daban-daban a jihar.

Sanarwar da kakakin rundunar, ASP Abubakar Sadiq ya fitar a yau Juma’a tace, an kama gungun ‘yan fashin ne a ranar 8 ga watan Satumbar da muke ciki, da misalin karfe 2 na rana, lokacin da jami’an ‘yan sanda daga yankin Funtua suka kai samame a bisa samun bayanan sirri.

Ya kara da cewa an yi nasarar kwato banduran atamfa 94 da leshi-leshi da bandura 2 na yadudduka, da aka kiyasta kudinsu zai kai naira miliyan 4 yayin samamen.

Har ila yau, rundunar ta cafke wasu mutane 3 da take zargi da mallakar bindiga kirar gida, a matsayin wani bangare na matakan da take dauka na karfafa aniyarta ta magance laifuffuka da tabbatar da zaman lafiyar al’umma.