‘Yan sandan suka ce an tsinci Hassan Zein jumma’ar nan a bayangarin birnin Kano, kuma lafiyarsa kalau.
WASHINGTON, DC —
‘Yan sanda sun ce sun gano wani Kwara dan kasuwa wanda aka sace a birnin Kano, cibiyar hada-hadar kasuwanci ta arewacin Najeriya.
Wani mai magana da yawun ‘yan sandan, ASP Musa Magaji Majiya, yace an samu Hassan Zein lafiyarsa kalau, bayan da aka jefar da shi jumma’ar nan a wajen birnin Kano.
A ranar litinin ne wasu ‘yan bindiga suka abka cikin kamfanin Mr. Zein, M.C. Plastic Co, suka yi awon gaba da shi.
Iyalansa suka ce ba a nemi su biya kudin diyya ba, kuma bas u biya ba, koda yake an saba neman kudin diyya kafin a sako mutanen da aka sace a Najeriya. Shi ma jami’in ‘yan sanda ASP Majiya, yace ba a biya diyyar ko kwabo ba.
Yace ‘yan sanda sun a ci gaba da binciken wannan lamarin, kuma babu wanda aka kama dangane da satar Kwaran.