Bayan babban kotun tarayya ta yi watsi da karar da aka shigar lauyan da ya shigar da karar a madadin jama'ar karamar hukumar Jos Ta Kudu Ahmaed Garba ya ce zasu daukaka kara.Kotun ta yi watsi da karar ne bisa ga dalilin rashin gamsassun hujjoji daga masu shigar da karar.
A farkon wannan makon ne babban kotun dake Jos ta yi watsi da karar da wasu mutane suka shigar inda suke tuhumar tsohon shugaban 'yansandan jihar Filato Gregory Anyatim da gidan rediyo da na teleibijan mallakar jihar Filato bisa ga bayanan da kwamishanan 'yansanda na wannan lokacin ya yi kan musabbabin tashin rikicin yankin St Michael dake cikin birnin Jos wanda rediyo da telebijan suka dinga yayatawa. Masu shigar da kara sun ce yayatawar ce ta yi sanadiyar rura wutar rikicin da ya kai ga rashin rayuka da dama a karamar hukumar Jos Ta Kudu.
Lauya Ahmed Garba shi ne jagoran masu shigar da karar ya yi bayani kan yadda ta kaya a kotun. Ya ce sun kwashe wajen shekara uku suna kan shari'ar. Ya ce yanzu kotu ta yanke hukunci inda ta ce bata gamsu da muhawarar da su dake jagorantar masu shigar da karar suka bayar ba.Kotun ta ce furucin Mr. Gregory Anyatim ya yi ne a cikin yanayin aikinsa kuma ba ya yi ba ne da wata mummunar manufa ba.Ya ce amma sun riga sun yanke shawara zasu tafi kotun gaba inda zasu kalubali hukuncin. Ya ce zasu bi matakin shari'a har zuwa kotun koli na kasar. Idan a kotun koli basu yadda da abun da suke fada ba to sai su barwa Allah.
To amma da aka fadawa Ahmed Garba cewa shi Gregory Anyatim ya rasu sai ya ce babu wani bayani da aka gabatar a gaban kotu cewa ya rasu. Ya ce bashi kadai suke kara ba. Suna karar hukumar da ta daukeshi aiki. Kan ko suna neman diya sai ya ce abun da suke nema nera miliyan dubu daya ne saboda asarar dukiya da rayuka da aka yiwa mutanen Kuru Karama da sauran kauyuka dake kewaye da su.
Da yake mayarda martani kwamishanan yada labarai na kihar Filato Yiljap Abraham shi ne shugaban gidan rediyo da telebijan mallakar jihar a wannan lokacin ya ce kodayake kotu ta yi watsi da karar lokaci ne da yakamata a manta da abubuwan da suka faru a can baya domin samun zaman lafiya mai dorewa. Ya ce alkalin kotun ya ce yadda suka yi aikinsu ya bi tsarin aikin gidan jarida. Dangane da daukaka karar da masu shigar da kara suka ce zasu yi Mr Abraham ya ce suna da 'yancin su yi hakan. Amma maimakon a cigaba da tunashe da mutane kan abubuwan da suka faru da yakamata su sa idanu kan gaba. Allah ya riga ya kaddara wasu abubuwa zasu faru kuma mutum bashi da iko a kansu.
Zainab Babaji nada karin bayani.