Duk da shirye-shiryen gudanar da babban zaɓen Najeriya a baɗi, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasar (INEC) ta ce ta shirya tsaf don ganin ta gudanar da sahihin zaɓen gwamna a jihar Ekiti dake kudu maso yammacin Najeriya.
Yayin jawabinsa a taron masu ruwa da tsaki kan zabe a Ado-Ekiti babban birnin jihar, shugaban na INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya ce hukumarsa za ta tabbatar kuri'ar mutane ita ce za ta baiwa duk wanda ya ci ba tare da aringizo ko magudin zaɓe ba.
Jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin Najeriya, na cikin jihohi shida da ake gudanar da zaɓe ba lokacin babban zaɓe ba.
A ranar Asabar mai zuwa ce dai masu zabe za su je rumfunan zaɓe a jihar don zaɓan gwamnan da zai jagoranci jihar na shekaru huɗu.
Cikin shirye-shiryen ganin an gudanar da zaɓen lami lafiya hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, ta haɗa taron masu ruwa da tsaki kan harkokin zabe a Ado-Ekiti babban birnin jihar, don tattaunawa tare da baiwa juna shawara don ganin anyi zaɓen cikin kwanciyar hankali.
Yayin hira da Muryar Amurka Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya ce hukumarsa a shirye take don ganin an yi sahihin zaɓe.
A nasa ɓangaren, babban sufeta janar na ƴan sandan Najeriya Alkali Usman Baba ya ce, akalla 'ƴan sanda 17,000 ne za su yi aikin tabbatar da anyi zaɓen ba tare da wani tashin hankali ba.
‘Yan takara dama shugabannin jam'iyyu daban-daban sun nuna amincewarsu da shirye-shiryen hukumar zaben mai zaman kanta, duk da cewa wasu mazauna jihar na cikin zulumi saboda matsalar tsaro dake addabar jihohi masu makwabtaka da Ekiti.
Saurari cikakken rahoton Alhassan Bala:
Your browser doesn’t support HTML5