Shugaba Tinubu ya gabatar da bukatar ciwo bashin Naira Triliyan daya da biliyan saba'in da bakwai, wanda zai kawo jimlar bashi da ke kan Najeriya zuwa Naira triliyan 138.
Majalisar Dattawan Kasar ta amince da karbar bashin ba tare da yin wata mahawara ba. Lamarin da bai kwanta wa 'yan Najeriya a rai ba.
A hirar shi da Muryar Amurka, masanin tattalin arziki Shuaibu Idris Mikati ya yi tsokaci cewa, wannan bashi ba karamin tashin hankali ba ne, domin in har za a bi ka'ida ya kamata a fito fili a gaya wa 'yan Najeriya abubuwan da aka yi da kudaden da aka ciwo bashin su. Mikati ya ce Majalisa ba ta kyauta ba da ta amince da cin bashin ba tare da bin diddigin dalilan ciwo bashin ba.
A nashi nazarin, Shugaban Cibiyar Horon 'Yan Majalisa a Afirka da ke Abuja Forfesa Usman Mohammed ya ce akwai abin dubawa a wannan lamarin sosai da domin bisa ga cewarshi, an kai Kasar an baro, da yawan cin bashi.
Farfesa Usman ya bayyana cewa, daga zamanin tsohon Shugaban kasa zuwa wannan mulki na Tinubu, an ciwo bashin Naira Triliyan 133, amma ba a ga komi da aka yi da kudaden ba. Forfesa Usman ya ce dukanin fanonin gudanar da kasar da bashi ake gudanar da su wanda ya nuna cewa, an daure kasar da sarkar bashi wanda 'ya'ya da jikokin za su sha wahala wajen biya. Usman ya kuma shawarta cewa, ya kamata a yi binciken abinda ake yi da kudaden
Duk yunkurin Muryar Amurka na jin ta bakin yan Majalisar a lokacin hada wannan rahoton ya cimma tura, sa dai a wasikar da ya aika wa Majalisar Dattawan,Tinubu ya ce wannan bashi na dalar Amurka biliyan 2.2 zai yi amfani da shi ne wajen cike gibin kasafin Kudin wannan shekara na 2024.
Tuni Majalisar ta bada izinin a cigaba da kashe kasafin kudin shekara 2023 har karshen watan Disamba mai kamawa.
Bankin Duniya ya ce Najeriya ita ce kasa ta uku a cin bashi, kuma bincike da Ofishin Kula da Basussuka ya yi, ya nuna cewa, an ci bashin da ya kai Naira Triliyan 50 a cikin wattani 19 da kama aikin gwamnatin Tinubu.
Saurari cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5