Ya Kamata 'Yan Najeriya Su Nemi Bayani Daga Buhari Game Da Rashin Tsaro a Kasar -Shi'a

Sheikh Ibrahim El Zakzaky, Shugaban 'yan Shi'a.

Kungiyar mabiya akidar Shi’a a Najeriya ta Islamic Movement in Nigeria, IMN, ta ce ‘yan Najeriya su nemi bayani daga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a kan tabarbarewar tsaro a cikin kasar.

Kungiyar ta IMN ta ce a lokacin mulkin Shugaba Jonathan, Buhari da wasu manyan mukarrabansa ne su ke sahun gaba wurin neman Jonathan ya yi murabus sakamakon gaza magance matsalar tsaro a wancan lokacin.

Wata sanarwar da Shugaban kungiyar da Sashen Labarai na IMN, Ibrahim Musa ya sanya wa hannu a Kaduna a yau Talata na cewa, “lokaci ya yi da ya kamata ‘yan Najeriya su nemi bayani daga gwamnatin Buhari a kan tabarbarewar tsaron kasar, musamman a arewacin kasar, kana a dora mata alhakin faruwar haka.

Karin bayani akan: Zaria, Boko Haram, Sheikh Ibrahim El Zakzaky​, Shi'a, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

“A lokacin gwamnatin Jonathan, Buhari da shi da mukarrabansa da suka nemi Jonathan ya yi murabus saboda lalacewar tsaro a wancan lokaci, mun yi al’ajabin yanda wannan gwamnati ta yanzu ta yi kunne uwar shegu a kan irin yadda su ka yi a baya.”

Kungiyar ta bayyana damuwa a kan yanda gwamnatin yanzu ba ta kimanta rayuwar bil Adama kuma tun kisan kare dangi na Zaria a shekarar 2015 inda, a cewarsu, rayuka sama da dubu su ka salwanta, wasu dubbai sun jikata kana aka lalata kadarori na miliyoyin Naira.

Sanarwar ta ce tun da yake batun tsaro ake yi, wajibi ne su fito su karyata hoton bidiyo na minti tara da ake yadawa wanda Sashen Labaran WION, na wani kamfanin Indiya na kasa da kasa mai labaran harshen Turanci mallakar Essel Group ya bayar a kan kafar Zee Media, da ke bayani game da ayyukan ta’addanci a Najeriya musamman a kan ayyukan Boko Haram da ‘yan bindiga.

Sanarwar ta ce kusan dukkannin bayanan cikin bidiyo game da batutuwa da aka yi gaskiya ne dari bisa dari, ammam kuma ta ce a karshe sai aka kara sunan kungiyar ta IMN daya daga cikin kungiyoyin ta’addanci tare da Boko Haram mara imani.

Kungiyar IMN ta ce me zai sa wanda ya hada hoton bidiyon ya yi wannan kuskure, ta na mai cewa Boko Haram da Islamic Movement of Nigeria mutane ne da su ka sha banban wurin koyarwa da akida.

A dan haka IMN, ta maimaita kira da ta saba a kan sake shugabanta, Sheikh Ibrahim El Zakzaky​ ba tare da wani sharadi ba da matarsa da wasu daruruwan magoya bayansa da ake ci gaba da rike su, tana mai cewa wannan kadai ne zai sa duniya ta amince za a tabbatar da adalci ga mutanen da sojojin Najeriya suka kashe su a shekarar 2015 a Zaria.