Fadar gwamnatin Najeriya ta ce ba ta da ikon da za ta sa a saki shugaban ‘yan Shi’a Sheikh Ibrahim El Zakzaky, tana mai ta wanke kanta daga zargin da ake yi cewa ta ki bin umurnin kotu.
Wata sanarwa dauke da sa hannu mai ba Shugaba Muhammadu Buhari shawara kan harkar yada labarai, Garba Shehu, wacce Muryar Amurka ta samu, ta nuna cewa ba hurumin gwamnatin tarayyar ba ne ta sa a sake shugaban ‘yan Shi’an.
“A iya sanin ma’aikatar shari’ar kasar nan, ba mu da hurumi a shari’ar El Zakzaky. Gwamnatin tarayya ba ta da hannu a wannan batun.” Sanarwar ta bayyana.
Saboda haka, fadar ta shugaban kasa ta yi kira ga mabiya Shi’a, da su daina zangar zangar da ke ta da husuma, “su jira matsayar da kotu za ta dauka a Kaduna, inda a can ne ake shari’ar.”
Sanarwar ta kara da cewa, “kuskure ne a ce sun je kotu kuma suna ta da husuma domin neman adalci ga wani da ake zargi.”
Kotu Ta Dage Karar El Zakzaky
A karshen makon nan wata kotu a Kaduna ta dage sauraren shari’ar da lauyoyin malamin suka shigar zuwa karshen watan nan, wacce ta nemi a ba shi dama ya yaje kasar waje ya ga likita.
Jagororin kungiyar ta Shi’a, suna zargin cewa hukumomin sun hana likitoci su ga shugaban nasu, lamarin da ya sa lafiyarsa take ta tabarbarewa.
Rahotanni sun yi nuni da cewa malamin Shi’ar yana fama da matsananciyar rashin lafiya yayin da hukumomi suke tsare da shi.
Tun a Shekarar 2015 Aka Kama El Zakzaky
Hukumomi na tsare da Sheikh El Zakzaky tun a shekarar 2015 bayan wata tarzoma da ta tashi tsakanin mabiyansa da wata tawagar sojojin Najeriya, bayan da aka hana dakarun wucewa ta wata hanya da mabiya Shi’a ke wani taro.
Rahotanni sun ce a cikin tawagar da ta so wucewar a lokacin, har da babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai.
Kungiyar ta Shi’a, ta zargi dakarun Najeriyan da kashe mata daruruwan mambobi a wannan lokaci, ciki har da wasu daga cikin ‘ya'yan El- Zakzaky da kuma rusa mai gida.
A baya wasu kotunan kasar sun ba da umurni a sake shi a kuma biya shi diyya tare da gina mai gida, amma hukumomin sun ci gaba da tsare shi da uwargidansa, lamarin da ke ci gaba da haifar da zanga zangar neman ganin hukumomin sun bi umurnin kotunan.
Ko a makon da ya gabata, sai da aka yi wani artabu da mabiya Shi’a da jami'an tsaron a Abuja a lokacin da mambobin kungiyar suka je kofar majalisar dokokin kasar domin yin zanga zanga.
Rahotanni sun ce mutane da dama sun jikkata, ciki har da jami'an tsaro da kuma mambobin kungiyar ta Shi'a.