Lamarin tsaro ya kazanta a kasar ta yadda a wasu wurare al’umma sun kauracewa gidajensu saboda fargabar abin da zai iya faruwa da su.
Wasu an kashe ‘yan’uwansu an lalata dukiyoyinsu, hanyoyi da dama ba sa biyuwa, saboda satar mutane don neman kudin fansa da sauran matsalolin da basu kirguwa.
Mr. Mark Amani da ke sharhi kan lamuran tsaro ya ce abin takaici shi ne yadda masu rike da madafun iko a Najeriya ke rikon sakainar kashi wa lamuran na tsaro.
Alhaji Muhammad Yaro kuwa cewa ya yi ganin yadda ake kashe mutane ba kakkautawa a wasu wurare, dole gwamnati ta dauki matakan kara daukan jami’an tsaro don su kare jama’a.
Ita ma Hajiya Binta Musa Kabir dake aikin wanzadda zaman lafiya a Najeriya ta gargadi matasa ne da su guji shiga bangar siyasa.
Hukumomin tsaro a Najeriya sun ce suna iya bakin kokarinsu wajen ganin sun shawo kan wannan lamari yayin da shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashin zai mika kasar ga wanda zai gaje shi cikin yanayi na cikakken tsaro.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5