Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Sojojin Najeriya Biyu, An Nemi Wasu Shida An Rasa A Taraba


Yan bindiga
Yan bindiga

Wasu yan bindiga sunyi sunyi wa sojojin Najeriya kwanton bauna inda suka kashe biyu kuma a nazaton sun tafi da guda shida daka cikin sojojin a yankin Jamaga dake karamar hukumar garin Lamido a Jihar Taraba.

TARABA, NIGERIA - Wani matashi ne mazunin yankin da abin ya faru kuma yana daya daga cikin wanda ya sha da kyar yayin aukuwar lamarin, da alkawarin ba za a ambachi sunansa ba, ya shaidawa Muryan Amurka cewa a yanzu haka dai ‘yan bindiga sun maida yankunan karamar kasuwa.

Wani tsohon dan majalisa mai wakiltar garin Lamido na daya Alhaji Tanko Bobbo Andami, ya ce suna neman agaji daga gwamnatin tarayyar Najeriya da na Jihar Taraba akan wannan matsala da ta addabi yakin nasu.

Ya kara da cewa, yanzu haka manoma ba su isa su yi noma a yankin gaba daya ba, wadanda suka yi shuka kuma ba su iya zuwa gonakin ba suna cikin tashin hankali sosai.

Ana su bangaren gwamnatin Jihar Taraban kuwa ta bakin Kwamishinan riko na ma’aikatar yada labarai na Jihar Alhasan Hamman Gassol cewa ya yi lallai gwamnatin Jihar ta san da batun.

Kazalika Sakataren gwamnatin Jihar ya kira taro da shugabannin ‘yan banga da masu sa-kai don lalumbo hanyar da za su taimaka domin ganin an shawo kan wannan matsalar da ta-ki-ci-ta-ki- cinyewa a Jihar ga badaya.

Saurari rahoto cikin sauti daga Lado Salisu Muhammad Garba:

‘Yan Bindiga Sun Kashe Sojojin Najeriya Biyu, An Nemi Wasu Shida An Rasa A Taraba
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG