Matsalolin yin sabon fasfo ko sabuntawa ya shiga wani yanayi ne bayan bullar cutar koronabirus da ta kawo cikas ga komai a duniya tun shekarar 2020. Lamarin dai ya kara tsananta ne daga cikin shekarar 2021 inda yan Najeriya daga ciki da wajen kasar ke kokawa kan yadda yin sabon fasfo ko sabunta tsoho ke daukar akalla tsawon watanni 5 zuwa sama kafin su iya samun mafita.
Wani dan jarida da Muryar Amurka ta yi hira da shi, ya yi bayani a kan yadda neman sabunta fasfo din sa ya yi sanadiyar rasa wata damar zuwa kasar Amurka don samun neman horo.
A wani bangare kuma, wani magidanci mai suna Trust Idiong ya yi bayani a kan yadda ya dauki kusan watanni biyar kafin ya iya samun sabon fasfo bayan ya batar da nasa a jihar Legas.
Trust Idiong ya ce, “na batar da fasfo dina ne a watan Janairun shekarar 2022 a jihar Legas kuma na yi duk mai yiyuwa wajen sanar da hukuma kan lamarin tare da bin ka’idojin hukumar kula da shige-da-fice ta Najeriya amma na ji jiki inda ya dauke ni kusan watanni biyar na kusa rasa damar zana jarabawar IELTS wanda saura sa’a 48 wa’adin rubutawa ya kare kafin na sami fasfo dina a ranar 29 ga watan Mayun shekarar nan.”
Kakakin hukumar kula shige da fice ta Najeriya, mataimakin kwanturola Amos Okpu, ya bayyana cewa a shekarar 2021 sun fitar da tsarin samun sabon fasfo na makonni 6 inda ake daukan makonni 3 a wajen aikin sabuntawa baya ga mai nema ya cika sharadin shigar da bayanansa ta yanar gizo.
A makon da ya gabata, mukaddashin hukumar shige da ficen Najeriya, Isah Idris, ya bayyana cewa sun fitar da sabon tsarin sa ido kan yanayin sabunta ko yin sabon fasfo ga masu nema don saukake aikin a wata zantawa da ya yi da manema labarai a birnin Abuja.
Duk kokarin ji ta bakin hukumar dake bada katin shaidar zama dan kasa ta NIMC kan abun da take yi wajen hada gwiwa da hukumar NIS don samun bakin zare kan tsaikon da ake samu wajen tantance masu neman fasfo ya ci tura.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5