A yayin da Janar Buhari ya doke abokin takararsa na jam’iyar PDP, Goodluck Jonathan a babban zaben kasa da aka gudanar ranar asabar 28 ga watan Maris da ya gabata.
A wani rahoton wakilin sashin Hausa na muryar Amurka Abdulwahab Mohammad ya bayyan yadda jama’a da dama a jahohin Bauchi da Gombe ke tururuwa akan tituna suna rawa da kuma bushe-bushe.
Wasu kuma suna dauke da ruwa da tsintsiya suna zubawa a kasa suna wankewa. Wani daga cikin mutanen dake kade-kade da raye-rayen ya bayyana dalilinsa da kuma fatan su ga wannan sabuwar gwamnatin,
“Ina mai matukar farin ciki kwarai musamman yadda kowa da kowa hatta mata da kananan yara duk sun fito domin taya wannan sabuwar gwamnati murna, kuma muna farin ciki kwarai domin zai kawo mana sauyi.”
Fatan jama’a da dama a wannan lokaci shine, kawo karshen zubar da jinin da ake fama dashi dangane da hare haren kungiyar Boko Haram mai tada kayar baya a wasu jahohin Arewa maso gabashin Najeriya.
Your browser doesn’t support HTML5