Mutum 15 a hukumance suka rasa rayukansu yayin da aka kammala jigilar alhazan Najeriya 51,000 zuwa gida daga Makkah.
Da yake bankwana da sauran jami’an hukumar alhazan NAHCON a ofishin hukumar a Makkah, shugaban hukumar Jalal Ahmad-Arabi ya ce hukumar ta fara duba irin kalubalen da aka samu a farko bisa rashin daidaiton canjin Naira zuwa dalar Amurka.
Jalal-Arabi ya nuna fatan yin sabon shiri da wuri don fuskantar aikin hajjin 2025 ta hanyar magance matsalolin da aka fuskanta
“Da gaske ne an fara tangal-tangal abun kamar ba za ta mike ba amma da shi ke mun tsaya tsayin daka tun a na mutum a'a dubu goma dubu ashirin dubu 51 suka zo ta fannin gwamnati”
Babban likitan alhazan Dokta Abubakar Adamu Isma’il ya yi bayanin alkaluman da aka tattara bayan kammala aikin hajjin na wadanda a ka rasa inda ya tabbatr cewa “jimilla gaba daya in ka hada da Madina da Makkah da Masha’ir mutum 15 kenan.
"In ka tuna lokacin da mu ka kira taron manema labarai kafin Arafat mutum 12 yanzu ga 3” in ji likitan.
Ya kara da cewa cikin wadanda su ka mutu har da matar nan da ta fado daga gidan sama a Madina.
Your browser doesn’t support HTML5