'Yan Mata Adon Gari - Inji Samari

Kamar yadda shirin samartaka ya saba jin ra’ayoyin matasa akan abubuwan da suka shafi rayuwar su ta yau da kullum musamman harkokin soyayya, a wannan lokacin mun fara jin tabakin samarin ne akan kwalliya da ‘yan mata kan yi musamman ma ta gargajiya wadda suke yi da lalle wato kumshi.

Mata ‘yan kwalliya ne a cewar wasu daga cikin samarin kuma dan haka kamar yadda masu iya magana suka ce idan kana da kyau to ka kara da wanka. Dan haka a cewar su wajibi ne idan mace tana so ta sami karbuwa cikin tsararrakin ta, to ta kasance mai kula da kanta.

Abin tambaya a nan shine, kowane namiji ne ke ra’ayin irin wannan kwalliya? Amsar da wasu daga cikin ayarin samarin suka bada ita ce, yawan kwalliya ke sa wasu matan shiga matsaloli irin su yaudara, kwadayin abin duniya da sauran su, dan haka mace ta kasance mai tsabta kawai ma ya gamsar da su.

Daga karshe sun bayyana cewa yawan kwalliya ke sa wasu ‘yan mata zama masu kishi da rashin rikon amana domin idan basu da kudin da zasu dauki dawainiyar canza kwalliyar akan lokaci, sai su fara canza tunani.

Menene ra'ayin ka akan wannan? garzaya shafin mu na facebook domin bayyana ra'ayi.

Ga cikakkiyar hirar.