‘Yan Majalisun Nigeria Matasan Jam’iyyar APC Sun Yi Taron Goyon Bayan Shugaba Buhari A Kaduna

Shugaba Muhammad Buhari da matasan 'yan majalisun jihohin arewa maso yammacin Nigeria da Kaduna suka yi taron mara masa baya akan zaben 2019

Wasu ‘yan majalisu, ‘yan jam’iyyar APC matasa daga majalisun tarayya da jihohi sun yi taron marawa Shugaba Muhammad Buhari baya domin ya ci zaben shekarar 2019

Duk da rarrabuwar kawunan da ta addabi jam’iyyar APC da ta kai ga rabuwa gida biyu, wasu ‘yan majalisu matasa magoya bayan shugaban kasa Muhammad Buhari sun yi taro a Kaduna.

A wurin taron matasan sun fada cewa rarrabuwar ba zata kawo wata barazana ba ga nasarar shugaban a zaben shekarar 2019.

Dan Majalisar Yusuf Bala Ikara daga jihar Kaduna ya ce tashe tashen hankulan da ake samu wasu ne ke hadda su da gangan. Yace duk mai hankali ya san matsalolin tsaro da ake fuskanta wasu ne da suke ganin dama ta kubce masu basa son kasar ta zauna lafiya. Su sun sani shugaban kasa ya yi duk abun da zai yi ya samar da tsaro. Ya kara da cewa a can baya kananan hukumomi 12 ‘yan Boko Haram ke rike dasu amma yau basu rike da ko daya. Ya ce matsalar tsaro ma a jihohin Binuwai, Plato, Zamfara da dai sauran wurare da yaddar Allah zasu magance ta.

Sanata Abu Ibrahim daga jihar Katsina wanda ya shugabanci taron., yace cewa gwamnatin ta yi aiki, ayyuka kuma masu kyau. Saboda haka ya cancanta a ba shugaba damar ci gaba da aikinsa. Haka kuma ‘yan majalisun sun ce ya kamata shugaban kasa ya yi anfani da darajarsa ya kawo masalaha tsakanin wadanda ke da matsaloli a tsakanin su.

Mataimakin gwamnan jihar Kaduna Mr Barnabas Bala Banti shi ya wakilici gwamnan jihar a taron a matsayin mai masaukin baki. Yace jihar Kaduna na kan gaba wajen amincewa da ayyukan Shugaban kasa wanda shi ma mazaunin Kaduna ne..

Dan Majlisa Abubakar Yahaya Kusada daga jihar Katsina, wanda kuma shi ne shugaban majalisar dokokin jihar, ya ce su ‘yan majalisun dokokin jihohi da tarayya masu shekaru kasa da 45 suka ga lokaci ya yi su yi karatun ta natsu dangane da irin gudummawar da zasu ba shugaban kasa domin ganin cewa ya sake komawa kan kujerarshi a shekarar 2019. Suna ganin tsare tsaren da shugaban ya fara zasu kai kasar tudun muntsira matasa kuma zasu anfana.

Shi ma Malam Samaila Suleiman, wakilin karamar hukumar Kaduna ta Arewa ya ce abun da ya jawo hankalinsu shi ne shugaban kasa da mataimakinsa ba matasa ba ne amma kuma a zuciya matasa ne. Duk manufofinsu an ginasu domin ci gaban matasa ne. Basu da hujjar kin fitowa su kira mutane su marawa shugaban kasa baya.

Taron matasan ‘yan majalisun ya samu halartar wakilai daga duka jihohin arewa maso yamma da Kaduna

A saurari rahoton Isa Lawal Ikara

Your browser doesn’t support HTML5

‘Yan Majalisun Nigeria Matasa Daga Jam’iyyar APC Dake Goyon Bayan Shugaban Kasa Sun Yi Taro A Kaduna – 4’ 03”