Wasu ‘yan jam’iyyar a karkashin shugabancin Alhaji Buba Galadima sun kafa wani bangaren jam’iyyar da suka kira Reformed APC a turance wato Gyararriyar APC, ko kuma APC da aka yiwa garambawul
Bangaren na Buba Galadima ya kira taron manema labarai a Otel din Sheraton a Abuja jiya inda shugaban ya bada dalilin da ya sa suka dauki matakin tar da samun mu'abayar shugaban PDP da ta narke zuwa cikin APC a shekarar 2015 Kawu Baraje.
Yace watani biyu da suka shige akwai korafe korafe da yawa. Mutane da yawa sun je kotu amma ba’a yi musu adalci ba. Ba’a nuna gaskiya ba akan yadda aka fitar da shugabanin jam’iyyar.
Y ace su kuma a matsayin wadanda suka yi sadarkarwa suka kafa jam’iyyar tilas ya wajaba a kansu su fito su yi gyara in ana so ko ba’a so saboda jam’iyyar ba ta mutum daya ba ce. Jam’iyya ce ta al’umman Nigeria.
Ya ci gaba da cewa wannan yaki na gyara jam’iyyar shi ne suka sa a gabansu. Zasu ci nasara saboda al’umma sun san abubuwan da suke yi, suna yi ne ba domin son kansu ba ne.
Alhaji Buba Galadima yace zaben 2019 ba mai samun nasara sai adali, mai kamanta Gaskiya sai kuma mai kula da wadanda suka yi masa wahala.
A saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya
Facebook Forum