'Yan Majalisun Amurka da Yarjejeniya kan Shirin Nukiliyar Iran

Sakatarori uku da suka bayyana a gaban majalisun Amurka.

Sakataren harkokin tsaron Amurka da na tsaro da na makamashi zasu bayyana gaban 'yan majalisu saboda kare yarjejeniyar da aka cimma akan shirin nukiliyar Iran

Yau Laraba wasu 'yan majalisar dokokin Amurka, zasu sami damar sauraro da kuma yin tambayoyi ga manyan jami'an Amurka, a ci gaba da kokarinsu na tantance yarjejeniyar kasa -da-kasa a ka kulla da Iran kan shirin Nukiliyarta.

Sakataren harkokin wajen Amurka John kerry, da takwaransa na tsaro Ashton Carter, da sakataren makamashi Ernest Moniz, da kuma babban hafsan hafsoshin Amurka Martin Dempsey, zasu bayyana a gaban kwamitin kula da harkokin soja na majalisar Dattijai. Zaman zai fi maida hankali ne kan yadda yarjejeniyar zata "shafi muradun Amurka, da kuma daidaiton karfin soja na kasashe dake gabas ta tsakiya".

Majalisun dokokin Amurka suna da wata biyu domin su tantance yarjejeniyar kan shirin Nukiliyar Iran, saboda haka kwamitoci a majalisun biyu, suna yin tambayoyi ga manyan jami'an gwamnatin shugaba Obama, musamman sakatare Kerry, da kuma Moniz, wadanda suna daga cikin tawagar da ta cimma yarjejeniyar a farkon wannan wata.