'Yan Majalisar Wakilan Amurka Na Democrat Sun Kawo Karshen Zaman Dirshan

'Yan Democrats yayinda suke zaman dirshan cikin zauren Majalisar Wakilan Amurka

‘Yan majilisar dokokin jamiyyar Democrat na nan Amurka sunyi ta sowa wa ‘yan uwan su na jamiyyar Republican, bayan sun kawo karshen zaman dirshan da sukayi na saoi’I 26 a wajen zauren majilisar da ake kira CAPITOL.

Dan majilsa John Lewis, wanda sananne ne wajen kare hakkin bil adama shine ya jagoranci ‘yan jamiyyar ta Democrat ficewa zauren majilisar inda magoya bayan su suka kewaye su suna sowa suna mun gode mun gode.

Daga bisani kuma ‘yan majilisar sun barke da sowa a komawa cikin zauren majilisar inda kuma suka ci gaba da rera taken kare hakkin bil adama, suna cewa zamu shawo kan al’amarin. Sai dai wannan karon sun kara da cewa zasu haki gaba domin ko sai sun tabbatar an samar da wannan kudirin.

'Yan Democrats suna waka mai taken "Zamu Ci Nasara"

Sun kammala wakar dai ne a tsawon rana guda wanda shine irin sa na farko da majilisar wakilan ta Amurka, inda ‘yan jamiyyar Republican suka kashe naurar daukar hoto wanda ke nuna ayyukan dake gudana a Majilisa, wanda hakan ya tilasta ‘yan jamiyyar Democrat su koma ga anfani da hanoyin sadarwa ta zamani domin ganin sun aike da sakonnin su akan wannan zanga-zangar da suke yi.

‘Yar majilisa Debbie Dingell wadda ta taba huskantar barazanar ta'addanci game da bindiga ita ce tafi kowa nuna damuwar ta sailin da ake nuna ta kai tsaye lokacin dasuke zaman dirshan din.