‘Yan majalisar dattawa a Jamhuriyar Kamaru na ci gaba da zaman tattaunawa game da gyaran lamarin kasafin kudaden da za a kashe a kasar a shekarar 2016.
WASHINGTON DC —
Sun kwashe kwanaki goma suna ta faman tattauna yadda ya kamata a ce an aiwatar da hada-hadar kashe kudaden shekarar da za a shiga.
Har ma da maganar yadda za a inganta yadda kasar zata samu kudaden shiga daga cikin gida da kasashen ketare.
A karshe tattaunawar na son cimma matsaya da zata samarwa kasar ci gaba a bangarori daban-daban musamman kayan masarufi.
Wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka Muhaman Auwal garba ya aiko mana da wannan rahoton.
Your browser doesn’t support HTML5