Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Masana’antun Afirka Ta Duniya


Taswirar Kasashen Afirka
Taswirar Kasashen Afirka

Yau ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe a matsayin ranar Masana’antun Afirka. Taken ranar bana shine, “Amfani da Manya da Kananan Masana’antu a Samar da Ayyuka don Yakar Talauci”.

Abokin aikinmu Ibrahim Garba ya tattauna da wani matsakaicin masana’anci Alhaji Jibrin Tafida, don jin ci gaban da aka samu tsakanin ranar ta yau da bikin ranar da aka yi a baya a Amurka. Inda ya fara da cewa, masu masana’antu a nahiyar Afirka na fuskantar matsalolin bunkasar matsakaita da manyan masana’antu.

Sannan hakan na faruwa ne kasancewar duniya ta kara yawan jama’a da kuma kalubalen yanayi da makamantansu. Yayi kira ga gwamnatoci da su taimakawa matasa da mata game da samanr da ayyukan yi. Yace idan aka bawa mace aikin yi kamar k aba duk al’umma ne.

Idan kuma ka bawa matasa aikin yi, to ka taimakawa zaman lafiya, domin kuwa idan matasa ba s u da abin yi to komai na iya faruwa da yanayion tsaron kasa. Ana iya sauraron cikakkiyar hirar ta hanyar latsa maballin sautin da ke kasan labarin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG