ACCRA, GHANA - Da yake jawabi a taron kaddamar da kungiyar Think Progress Ghana, kungiyar da za ta yi nazari kan samar da hanyoyin magance kalubalen tattalin arziki a kasar da ma nahiyar Afrika baki daya, tsohon shugaban kasa John Mahama ya caccaki gwamnatin Nana Akufo-Addo a kan jefa kasar Ghana cikin wahala saboda yawan karbo basussuka daga kasashen waje.
Mahama ya ce ‘yan majalisar dokoki na jam’iyyar NDC ba za su goyi bayan duk wani rance “da bai da rangwame ko lamunin da ba za a yi amfani da shi wajen wani aiki da zai amfani al’ummar kasar ba. Ba za mu taimaka wajen kara tabarbarewar tattalin arzikin Ghana ba, wanda wannan gwamnati take da aniyyar yi”.
Akwai kudurin gwamnati na yarjejeniyar neman rancen dala biliyan daya daga bankuna, wanda ke jiran amincewar majalisar dokoki. Idan aka amince da kudaden, za a yi amfani da su wajen habbaka jari da kuma wasu kudade da za a kashe a cikin kasafin kudin shekarar 2022.
Wannan kira da John Mahama ya yi, ya samu martani daga mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin kasar Alexander Afenyo-Markin, wanda ya ce wannan kiran wani yunkuri ne na yi wa harkokin majalisa zagon kasa da kuma dabarar kawo cikas a kokarin gwamnati na farfado da tattalin arzikin kasar.
A wata hira da Muryar Amurka, Muhammad Nazir jami’in sadarwa na jam’iyyar adawa ta NDC ya kare matsayin tsohon shugaban yana mai cewa yana yi wa kansa shimfida ne don guje wa samun kansa dabaibaye da basussuka idan ya dawo kan karagar mulki.
Alhaji Aliyu Kabe, mamban tawagar jam’iyyar NPP mai ci, a nasa bangaren cewa ya yi a matsayinsa na tsohon shugaban kasa bai kamata ya fadi haka ba domin duk abinda gwamnati mai ci ke yi domin ci gaban kasa ne kuma shi ma ya bar bashi a lokacin da ya sauka daga mulki.
Malam Seeba Shakibu, shi ne babban sakataren jam’iyyar PNC reshen yankin Greater Accra, ya fadi cewa jam’iyyarsu ta amince da abinda John Mahama ya fada domin yanayin da kasar ke ciki sai da daukar mataki irin wannan.
Shi kuma dan jarida kuma mai fashin baki a kan al’amuran yau da kullum ya nuna cewa lallai tsohon shugaban kasar yana taka rawarsa ne wajen cika hakkin jama’a da ke rataye a kan jam’iyyar adawa, na kushe duk abinda zai yi illa ga jama’a da kasa baki daya.
A wani rubutu da tsohon shugaban kasa John Mahama ya yi a kafar sada zumunta, ya bukaci a sallami ministan kudi Ken Ofori-Atta kuma kada a sanya shi cikin wadanda za su tattauna da asusun lamuni na kasa da kasa domin a idon shi Ghana ta fuskanci "mummunan durkushewar tattalin arzikin kasa," a cewarsa.
Saurari cikakken Rahoton Idris Abdallah Bako:
Your browser doesn’t support HTML5