Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Ghana Za Ta Nemi Ceton Asusun IMF


Shugaban Ghana Nana Akufo Addo
Shugaban Ghana Nana Akufo Addo

Shugaban  Ghana Nana Addo Dankwa Akuffo Addo  ya baiwa ministan tattalin arzikin kasar Ken Ofori Atta, umurnin fara tattaunawa da asusun bada lamuni na kasa da kasa ta IMF, domin ceto kasar daga matsalar raunin tattalin arziki da ta ke fuskanta.

Kasar Ghana ta dauki matakin inganta dokar karbar harajin waya ta Elevy, domin samar da isashen kudaden shiga, abin da gwamnatin ke ganin zai sanya kasar dogaro da kai maimakon tuntubar kasashen waje domin neman tallafi, amma yunkurin bai haifar da sakamako mai kyau ba.

"Kashi goma cikin dari na kudaden da aka sa ran za a samu sakamakon karbar harajin E levy, ya gaza dan haka IMF ita ce mafita, " inji Garbi Ochere Darko, daya daga cikin jiga jigan jamiyyan NPP mai mulki.

Bayan fitar da sanarwar, babbar jam'iyyan adawa ta kasar NDC, ta ce tuntubar asusun IMF na tabbatarwa ba da wata shakka ba cewa gwamnatin Nana Addo ta nuna gazawa, inji Hon ABA Fesini wakilin jamiyyan NDC a Majalisar Dattawan kasar.

To sai dai da yake mayar da martani Hon Alexanda Afenyo Markin, wakilin jam'iyyar NPP mai mulki a Majalisar dattawan kasar ya ce gwamnati ta tunkari IMF ne sakamakon matsalolin da suka shafi duniya ciki har da korona tare da mamayar da Rasha ke yi a Ukraine

Dakta Najeeb Ibn Hassan, masanin tattalin arziki cewa ya yi zuwa hukumar IMF da kasar Ghana ta yi yana alfanu da rashin alfanu. Alfanu shine kasar za ta yi amfani da kudaden wajen magance matsalar dake damunta, kuma hukumar IMF kan iya yafe bashin. Rashin alfanu kuwa shine dole ne Ghana ta bi dukkan sharudan da aka gindaya mata.

Kasar Ghana na ckin jerin kasashen da ke fama da matsalar tattalin arziki sakamakon bular annobar coronavirus tare da mamayar da Rasha ke ci gaba da yi a Ukraine.

Saurari cikakken rahoton Hamza Adama cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

XS
SM
MD
LG