Ana kyautata zaton a yau Laraba ‘Yan Majalisar Dokokin Amurka zasu rattaba hannu akan amincewa da gagarumin takunkumi akan kasar Koriya ta Arewa, ‘yan kwanaki kadan bayan gwamantin ta Pyongyang ta gwada harba rokar da ka iya dakon makamin Nukiliya mai cin dogon zango, wanda ‘yan makonni ne tsakanin wani gwajin Nukiliyar da ta yi.
WASHINGTON, DC —
Wani dan jam’iyyar Republican Bob Corker kuma shugaban kwamitin huldar kasa da kasa na majalisar. Ya fadi cewa wannan kada kuri’a zai haye da dimbin kuri’un amincewa. ‘Yan Majalisar za su dakatar da tattauna kudurin dokar makamashi don su fuskanci maganar takunkumin na Koriya.
Kuma a kalla za su yi zaman mukabalar sa’oi 7 bayan sun gama kada kuri’unsu na kakaba takunkumin ga Koriya ta Arewa. Majalisar zata ma bukaci gwamnatin Obama da ta basu bayanin ko akwai hadin gwiwa tsakanin Koriya ta Arewar da kasar Iran a shirin Nukiliya.