Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Iraqi tayi ikirarin kammala kwace birinin Ramadi


'Yansandan kwantar da tarzoma na kasar Iraqi
'Yansandan kwantar da tarzoma na kasar Iraqi

Gwamnatin Iraq tace sojanta sun kamalla kwace garin Ramadi kwata-kwata daga hannun mayakan ISIS.

A yau Talata ne rundunar soja da ma’aikatar harakokin cikin gida na kasar suka bada sanarwar cewa sun gama kwace garin, har ma sun sake bude babbar hanyar nan ta Ramadi zuwa Baghdad.

A cikin watan Mayun bara ne dai mayakan ISIS din suka kwace garin na Ramadi, abinda ya zama babban abin kunya a wurin gwamnati.

Sai dai har yanzu sojan na Iraq na ci gaba da fama da jan aikin tonon nakiyoyi da bama-baman da mayakan ISIS din suka bizne ko ina a cikin garin.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG