Wasu 'Yan Majalisa Kan Bayyana Ra'ayin Tsayawa Takarar Shugaba Jonathan.

Ginin majalisun tarayyar Najeriya

Wadansu yan Majalisar Kasa sun bayyana ra'ayinsu a game da matakin da shugaban kasa ya dauka na bayyana niyar sa na tsayawa takara a zaben shekara 2015 a daidai lokacin da kasar ke cikin halin kakanakayi.

Ayayin da wadansu ke kuka da nuna alhini na rasa ‘ya’yansu da ‘yan uwa, awani harin kunar bakin wake daya auku jiya a Fataskum. Mahukuntan Najeriya na Dandalin Eagle square dake Abuja, inda a yau shugaban kasa Goodluck Jonathan ke bayyana niyarsa na sake tsayawa takara a zaben shekara ta 2015.

Dan Majalisar dattawa daga jihar yobe, sanata Alkali Abdulkadir Jajere ya bayyana ra’ayinsa kan shugaban kasar, inda yake cewa, “gamu mutanen Yobe da mutanen arewa maso gabashin Najeriya, dakuma ‘yan arewa gabaki daya, munyi tir da wannan kaddamar da kansa dayayi cewar zaiyi takara.”

Wannan lamarin dai yazone mako guda bayan wani dan kunar bakin wake ya kashe ‘yan shi’a ashirin da daya masu muzaharar Ashura agarin na Fatiskum.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Majalisa Kan Tsayawar Shugaba Jonathan - 4'10"