A birnin Abuja ‘yan kungiyar Islamic Movement of Nigeria wadanda aka fi sani da ‘yan Shi’a, sun gudanar da zanga zangar lumana, inda suka mamaye ofishin hukumar kare hakkin bil Adama, domin neman a sako musu shugabansu da hukumomin tsaron Najeriya ke tsare da shi.
Jagoran masu gangamin Abdullahi Mohammed Musa, yace anje an harbi jagoransu an ji masa rauni ta yadda yanzu baya iya gani da idonsa ‘daya, an kuma ajiye shi ba tare da an gurfanar da shi gaban kotu ba bayan ance bai yi wani laifi ba.
Yace hukumar kare hakkin bil Adama ta Human Right, har yanzu bata tabuka komai ba duk da cewar ‘yan kungiyar sun ziyarci hukumar lokuta da dama, hakan yasa suka sake dawowa domin ganin hukumar ta dauki mataki kasancewar babu wata doka da ta tanadi rike mutum ba tare da an gurfanar da shi gaban kotu ba.
Shi kuma daya daga cikin jagorin zanga zangar Muhtar Abdurrahman Awwal, ya nuna takaicin yadda hukumar kare hakkin bil Adama ta Najeriya, ta dauki matakin gaggawa yayin da babban hafsan sojan Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai ya kawo kukan cewa ‘yan Shi’a sun tare masa hanya a Zariya, amma sai gashi suma sun kawo kukansu wata da watanni ana ta jan kafa.
Sai dai kuma babu wani jami’in hukumar kare hakkin bil Adama da ya yarda yayi magana, kuma jami’ar hulda da ‘yan jaridu ta hukumar tace babban sakataren hukumar ne kadai ke da ikon yin magana da ‘yan Jaridu.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5