Da Hillary Clinton ta ci zaben da ta zama mace ta farko da zata zama shugabar kasa mafi arziki da karfi a duk fadin duniya.
Matan da suka yi juyayin rashin nasarar Hillary Clinton a Abuja suna ganin nasar Hillary Clinton ka iya bude wani sabon babi da zai karawa mata hanyoyin cigaba da taka rawa a siyasar duniya da ma nahiyar Afirka.
Matan na ganin hankoronsu na taka rawa a harkokin duniya zasu tabbata da nasarar Hillary Clinton wai idan aka yi la'akari da yadda mace ke shugabancin kasar Birtaniya da kuma kasar Jamus inda Angela Merkel ke jan ragamar shugabancin kasar..
Mariam Ibrahim Baba shahararriyar 'yar siyasa a Najeriya tace da Hillary Clinton taci zaben da an ga abun mamaki a duniya to sai dai abun da Allah ya tsara haka zai kasance, inji Mariam. Tace gaskiya ita bata ji dadi ba.
Haka ma Hajiya Fati Paris ta bayyana ra'ayinta akan zaben. Tace tunda mace ta fito a Amurka babu abun da ya saura. Matan Najeriya dole su fito su ma su tsaya takarar shugabancin kasar. Ta kira mata kada su ja da baya domin, wai lokacinsu ne. Tace maza kansu da kansu suke rayawa.
Imrana Wada Nas shugaban matasa yace siyasa tamkar mace ce da ciki ba'a san abun da zata haifa ba. Yace 'yan takaran karfinsu ya zo kusan daya dalili ke an da sakamakon ya ba mutane mamaki, amma injishi shi baya cikin mutanen da abun ya samesu bazata. Tun can farko shi baya son taci zaben saboda, wai bata dace da shugabancin kololuwa ba.
Shi ma Abubakar Sadiq mai sharhi akan lamuran siyasa ya marawa Trump baya amma da ya fi son Hillary Clinton ce taci zaben.
Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.