A cigaba da kai hare-haren da kungiyar Boko Haram ke yi a baya-bayan nan, tsattsaurar kungiyar ta auna wata cinkusasshiyar kasuwar kifi a jahar Borno, inda su ka hallaka mutane a kalla 18.
WASHINGTON D.C. —
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce wasu ‘yan kunar bakin wake su uku sun kai hari kan wata cinkusasshiyar kasuwar kifi, wadda da ke daura da birnin Maiduguri na arewa maso gabashin Najeriya da daren jiya Jumma’a, su ka kashe mutane 18 tare da raunata wasu 22.
Da misalin karfe 8:30 na dare agogon yakin, ‘yan kunar bakin waken su ka kai harin a garin Konduga, mai tazarar kilomita 25 a kudu maso Maiduguri, babban birnin jahar Borno.
Birnin Maiduguri, wanda nan ne mahaifar kungiya mai tsattsauran ra’ayin, ya zama turmin tsakar gida sha lugude ga wannan kungiya, wadda ta hallaka mutane sama da 20,000 tun daga 2009, ta kuma tilasta mutane sama da miliyan biyu barin muhallansu.
Mu na da karin bayani bayan labarai.