A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Borno, DSP Isoku, ya aikawa manema labari, yace akwai mutane uku da suka shiga dauke da bindigogi da bama bamai suna kokarin kutsawa garin Maiduguri, baki daya mutanen uku sun mutu, haka kuma sun kashe ma’aikacin Civilian JTF guda ‘daya a wajen tashar Muna.
DSP Isoku, ya kuma sake tabbatar da tashin bam ‘din unguwar Kalari, inda yace mutane hudu sun rasa rayukansu wanda suka hada da su ‘yan kunar bakin waken guda biyu.
Wakilin Muryar Amurka, Haruna Dauda, ya ziyarci unguwar Kaleri domin zantawa da mutanen da wannan iftila’i ya afkawa. A cewar Hassan Mandura, daya daga cikin mai gidan da ‘yan kunar bakin waken suka kaiwa hari gidansa, yace wata yarinya ce ta kwankwasa musu gida sai ‘yarsa ta je ta bude gida amma bata ga kowa ba sai aka ‘kara kwankwasa a zuwanta na biyun ne wata mata ta rungumi ‘yar sa bam ya tashi da su.
Shima Isah Abubakar, wanda ya tashi da wansa da suke uwa ‘daya uba ‘daya, yace sun sami labarin cewa na kwankwasa masa kofa ya kuma bude nan take bam ya tashi da shi.
Wakilin Muryar Amurka ya kuma zanta da Yahaya Ali, mutumin da Allah ya tserar da shi daga sharin maharan, ganin cewa sun kwankwasa masa kofa inda suka ce su ‘yan gudun hijira ne suna neman mafaka domin su kwana zuwa gobe, amma iyalensa basu bude kofarsu ba hakan yasa suka tafi.
Wannan dai ya zamanto wani sabon salo ne da ‘yan kunar bakin waken ke amfani da shi wajen kwankwasa mutane kofa musammam ma cikin dare su kuma yi kokarin kutsawa ko su tayar da bama baman dake jikinsu.
Your browser doesn’t support HTML5