‘Yan kudancin jihar Bornon, sun yi wannan kira ne a wani taron manema labarai da suk kira a jiya, na nuna kin amincewarsu da dakatar da tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar dattawan sanata Mohammed Ali Ndume, da suka ce ba a yi bisa ka’ida ba.
Tun daga lokacin da aka dakatar da wannan dan majalisa ne ake ta samun matsin lamba daga kungiyoyi masu zaman kansu da kuma gwamnatin jihar Borno, da ta yi tattaki a karkashin shugabancin gwamnan jihar Hon. Kashim Shettima, domin rokon majalisar dattawan ta janye wannan mataki da suka dauka.
Sai dai wasu kafafen yada labarai sun ambato shugaban majalisar dattawan na cewa wannan batu ya fi karfin sa.
Malam Yahaya Gaire, shine shugaban kungiyar kuma ya bayyana cewa shugaban kasa ya yi shiru akan wannan lamari, kuma lamari na siyasa bai kamata a yi shiru ba musamman idan an yi la’akari da masu kokarin kawo cikas ga wannan mulki na demokaradiyya.
Sannu a hankali dai wannan batu na kara zafi, ganin yadda ake samun karuwar mutane da kungiyoyi masu nuna kin amincewarsu akan matakin da majalisar ta dauka, da kuma barazanar yiwa wasu daga cikin wakilan nasu kiranye idan har ba a sami dai daiton wannan lamari ba.
Ga cikakken rahoton Haruna Dauda Biu daga Maiduguri.
Your browser doesn’t support HTML5