Koda shike irin wannan ganawa ba sabuwar abu bace domin kuwa dukkan bangarorin biyu, ‘yan jam’iyya daya ne dake mulkar al’umma daya, amma ana ganin ganawar ta zo a dai dai lokacin da ‘yan Najeriya, ke da bukatu da dama daga shugabannin biyu.
Bayan an kammala ganawar ne shugaban majalisar ya yi wa manema labarai jawabi inda ya bayyana cewa ya yiwa shugaba Muhammadu Buhari, bayani ne akan kasafin kudi da kuma sababbin dokokin da majalisa ta amince da su musamman akan sha’anin zabe.
To amma ko mai yasa ba a tattauna akan batutuwan da suka shafi majalisa ba, da kuma ja-in-ja dake ake da bangaren gwamnati? Tambayar da wakilin sashen Hausa na muryar Amurka, Umar Faruk Musa, Kenan ya yiwa kakaki a fadar shugaban majalisar dattawa Mohammed Isa Funtua, inda ya bayyana cewa shugaban kasa ya riga ya kafa kwamitin da zai fuskanci wannan lamarin.
Ga cikakken rahoton Umar Faruk Musa.
Facebook Forum