Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Kano Za Ta Aiwatar Da Shirin Gina Kasuwar Zamani


Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnatin Jihar Kano ta ce za ta aiwatar da shirin gina kasuwar zamani da gwamnatocin baya suka dauki aniyar gina wa a baya amma abin ya cutura bisa wasu dalilai na siyasa ko kuma wani yanayi.

Ana sa ran kasuwar za ta kunshi otel otel daban daban da rumfunan ajiye kayayyaki da kamfanonin sadarwa da sauran fannonin hada hadar cinikayya daban daban.

Aikin zai kasance na hadin gwiwa ne tsakanin gwamnatin jihar da kamfanoni masu zaman kansu.

To sai dai bayan samar da filin da za'a yi ginin ba'a kai ga fara aikin ba har gwamnatin Ibrahim Shekarau ta shude a shekarar 2011.

Ita ma gwamnatin Dr. Musa Kwankwaso ta ta da maganar kuma har ta kulla yarjejeniya da wani sabon kamfani amma tun ba'a je ko ina ba al'amarin ya tabarbare kana wa'adin gwamnatin ya kare ba tare da tabuka komai ba a fannin gina kasuwar.

Yanzu dai gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta sha alwashin yin aikin. inda Gwamnan ya ce har sun fito da sabon tsari bisa wata sabuwar yarjejeniya da wani kamfani.

Saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari domin jin cikakken bayani kan shirin gina kasuwar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG