‘Yan Kasuwa Na Korafin Rufe Kasuwar Wuse a Abuja

‘Yan kasuwa na kokawa kan rufe kasuwar Wuse, Abuja sakamakon yadda wasu ’yan kasuwa suka ki mutunta ka’idojin kare kai daga Coronavirus.

Bayan rufe kasuwannin Wuse, UTC da ginin Murg dake burnin tarayya Abuja sakamakon kin bin ka’aidojin kare kai daga cutar Korona, kananan ‘yan kasuwa na kokawa kan asarar da hakan zai ci gaba da jawo wa kasuwancinsu idan ba a bude kasuwannin, musamman na Wuse, cikin gaggawa ba.

Wasu daga cikin ‘yan kasuwan, kamar Auwal Abubakar sun bayyana irin tasirin da rufe kasuwar ke da shi ga sana’arsu. Ya ce rufe kasuwar ya kawo matsala a sana’ar sa ta sayar da kaji masu rai. Ya ce sukan je tun da sassafe don su bai wa kaji abinci kafin sayar da su, amma babu wani notis sai aka rufe kasuwar.

Shugaban kwamitin ko-ta-kwana a aiwatar da dokokin kare kai na birnin Abuja, Attah Ikharo, ya ce an rufe kasuwar Wuse ne biyo bayan umarnin kotun ko ta kwana da ta samu hukumar kasuwar, da ‘yan kasuwar ma da laifin keta dokar kare kai game da cutar coronavirus, kuma kasuwannin zasu kasance a rufe har sai lauyoyin kwamitin sun koma kotu don sake nazari inda ya bukaci mutane su bi doka ko ba hukuma a wajen.

Baya ga rufe kasuwannin dai, kotun ko ta kwanan da ta samu jagorancin mai shari’a Idayat Akanni, ta hukunta mutane kimanin 100 da aka kama da laifin keta dokar saka takunkumin fuska a bainar jama’a ta hanyar cinsu tarar naira dubu 2 kowannen su, wanda hakan na zuwa kasa da mako daya da shugaba Buhari ya rattaba hannu a dokar kare kai kan cutar coronavirus ta shekarar 2021 kuma hukumar babban birnin tarayya Abuja ta fara aiki a kai gadan-gadan.

A saurari rahoto cikin sauti daga Halima Abdulra’uf:

Your browser doesn’t support HTML5

‘Yan Kasuwa Na Korafin Rufe Kasuwar Wuse a Abuja