'Yan Kasashen Waje Da Suka Makale A Haiti Sun Kosa Su Samu Hanyar Barin Kasar

Yan sanda a Haiti

'Yan kasashen waje da dama, ciki har da Amurkawa da ‘yan kasar Canada sun makale a kasar Haiti, inda suke kokarin barin kasar mai fama da tashe-tashen hankula, inda kungiyoyin da ke adawa da gwamnati ke fafatawa da 'yan sanda, kuma tuni suka rufe filayen jiragen sama 2 na kasa da kasa na kasar.

Mutanen sun je Haiti ne bisa dalilai dabam dabam da suka hada da zuwa aikin bisharar mishan da na agajin jin kai. Yanzu, sun makale a otal-otal da gidaje, ba sa iya fita kasar ta jirgin sama, ko ta ruwa ko ta ƙasa, yayin da har yanzu harkoki suka durkushe a Haiti sakamakon tarzoma da buƙatun ƙungiyoyin da ke neman Firai Minista Ariel Henry ya yi murabus.

“Mun makale a kasar,” a cewar Richard Phillips, dan shekara 65 daga Ottawa babban birnin kasar Canada, wanda ya sha zuwa Haiti lokuta da yawa domin gudanar da ayyuka na Majalisar Dinkin Duniya, da USAID, yanzu kuma a matsayin ma’aikacin wata kungiya mai zaman kanta ta Haiti da ake kira Papyrus.

Bayan kammala aikinsa, Phillips ya shiga jirgin sama zuwa Port-au-Prince babban birnin kasar, amma yana isa ya tarar an soke tashin jirginsa. Ya sauka a wani otal da ke kusa, amma an yi ta harbe-harbe babu kakkautawa a wurin, don haka ya koma wani wuri mai dan kwanciyar hankali.

"A gaskiya mun damu matuka game da yadda lamarin ke tafiya," abin da ya fada wa Kamfanin dillancin labarai na Associated Press ta wayar tarho kenan. "Idan rundunar 'yan sandan ta kasa aiki, za a fuskanci tashe-tashen hankula a kan tituna, kuma ta yiwu mu kasance a nan tsawon wata daya ko fiye da haka."

An kashe mutane da dama a hare-haren kungiyoyin mayakan da aka fara a ranar 29 ga watan Fabrairu, kuma karin mutane fiye da 15,000 rikicin ya raba da gidanjesu.

Gwamnatin Haiti ta tsawaita dokar ta-bacin da ta ayyana da kuma dokar hana fita da dare a kokarin kwantar da tarzoma, amma duk da haka ana ci gaba da kai hare-hare.

Gungun bata gari sun kona ofisoshin ‘yan sanda tare da sakin fursunoni sama da 4,000 daga manyan gidajen yari biyu na kasar Haiti, sun kuma kai hari a babban filin jirgin saman birnin Port-au-Prince wanda har yanzu ke a rufe. A sakamakon haka, Firai Ministan kasar ya kasa komawa gida bayan wata tafiya da ya yi zuwa Kenya domin neman goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya don tura 'yan sanda daga kasar da ke gabashin Afirka.