Shugabanin jam’iyar sun kira wani taron manema labarai a jihar inda suka ce, ba a kyautata musu ba kasancewar ana baiwa wadanda basu bautawa jam’iya ba mukamai, yayin da su kuwa yan bangaren wanda aka mika sunan ke murna.
Da farko Shugaban jam’iyar a jihar Hassan Jika Ardo, yace “da farko ba mu san da wannan sunan ba har ga Allah, na biyu kuma mun sani cewa ba shugaba Buhari ne ya bada wannan sunan ba, domin mun sani cewa a lokacin da muka yi taro da shugaba Buhari a sakatariyar jam’iyar APC, ya bayyana mana cewa bazai yiwu ba ace mai zazzabi daban sannan mai shan magani daban.”
Shima da yake karin haske shugaban matasa na jam’iyar Abdullahi Ade, cewa yayi “Mu a jihar Taraba, ba ayi mana adalci ba, wanda aka bada sunansa ba dan jam’iyar APC bane. Mu ba zamu lamunta ba, ba kuma zamu bari ba. Ka ga yanzu muka kamala taron gaggawa, kuma mun dau matsayan cewa bamu amince ba.’’
To sai dai yayin da wasu ke kuka wasu kuwa murna suke irinsu Ismail Mai Hanci, dake cikin magoya bayan wanda aka tura sunan sa din, inda yace, “Mu abin farin ciki ne, domin an zabo jakada na gari. Kuma su da suke cewa sun yiwa APC aiki wanne aiki suka yi? Ko sun manta ne, cewa ko a lokacin zaben fidda gwani ba hanawa Buhari ganin wakilai suka yi bane, kuma ga shi har minista aka basu”
Kawo yanzu dai Najeriya bata da jakadu a wasu kasashe, yayin da tuni wasu da aka tura sunayensu, da suka hada da tsohuwar mataimakiyar gwamnan jihar Filato, Mrs Paulen Tallen, ke cewa akai kasuwa.
Your browser doesn’t support HTML5