Kimanin watanni ukku ke nan da babban hafsan sojojin kasa Janar Buratai ya sake bude hanya daga Maiduguri zuwa Gamboru Ngala inda akan baiwa direbobi da fasinjoji kariya.
Wadannan mutanen da suka nuna fushinsu sun ce sun kwashe kwanaki fiye da arba'in a tasha suna jiran rakiyar jami'an tsaro. Sun zargi sojojin da raka wasu manyan motocin da suke karban dimbin kudade daga hannunsu , kaman Nera 200,000 kan kowace mota. Kananan motocin da basu iya biyan kudin su ne aka bari, ba'a kula dasu ba.
Wani Baba Shehu yace su talakawa basu da 'yanci shi ya sa suka fusata suka nufi fadar Shehun. An tarasu a tasha amma kuma an manta dasu gaba daya. Yace yanzu sun yi kwana arba'in cikin tashar. Wasu sun sayar da kadarorinsu domin su ci abinci. Wasu kuma bara ma suka shiga yi domin basu da abun da zasu sayar.
Wani direba yace sun biya kudin pas na tafiya amma yau kwanansu arba'in da daya. Kowace karamar mota na biyan nera 3100 a matsayin kudin pas, wato takardar izinin tafiya. Yace mata da yara suna nan kara zube har ma wasu suna mutuwa saboda rashin ci da sha.
Sun roki Shehun Borno da babbar murya ya shafe masu hawaye. Suna son ya yiwa Janar Buratai magana ya taimaka.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.