Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Sokoto Ta Kaddamar da Dokar Ta Baci Kan Ilimi


Waziri Aminu Tambuwal, gwamnan jihar Sokoto
Waziri Aminu Tambuwal, gwamnan jihar Sokoto

Gwamnan jihar Sokoto Waziri Aminu Tambuwal 'yan watanni bayan an rantsar dashi ya ayyana dokar ta baci a bangaren ilimi a watan Disamban bara tare da yunkurin kai dokin gaggawa kan bangaren ilimi

Yanzu dai gwamnan ya aike da kudurin dokar zuwa majalisar jihar domin ta zama dokar jiha ta kuma samu kafuwa a yi aiki da ita.

Wannan matakin wani bangare ne na aiwatar da dokar ta baci a bangaren ilimin jihar. Dokar zata tabbatar cewa ilimi wani hakki ne na yara da dole ne a basu. Dokar ta tanadi hukumta duk wani aiki ko yunkuri na tauye wannan hakkin na yara.

Barrister Suleiman Usman kwamishanan shari'ar jihar shi ya wakilci gwamnati wajen gabatar da kudurin dokar wa majalisa. Yace gwamnan jihar yayi imani cewa ilimi shi ne babban abun da za'a iya barwa mutum tamkar gado. Ba yaro ilimi ya fi a bashi dukiya. Ilimi haske ne, yana haskaka rayuwa. Ilimi shi ne fitilar duniya.

Ilimi, kiwon lafiya da muhalli suna cikin hakkokin 'yan Adama inji Barrister Usman. Amma wai saboda matakin jihar bai kai nan ba aka fara da ilimi a matakin farko.

Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:58 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG