Wannan sanarwa da mayakan suka fitar, na zuwa ne sa’oi kadan bayan da jiragen yakin dakarun da Saudiyyan ke jagoranta suka kai wani samame kan gidan tsohon shugaban kasar, Ali Abdullah Saleh, da ke Sana’a, babban birnin kasar.
Babu dai rahotanni da ke cewa Mr Saleh ya na gida a lokacin samamen.
A makon da ya gabata, Amurka da Saudiyya suka bayyana shirin tsagaita wuta na tsawon kwanaki biyar a Yamal, inda dakarun da Saudiyan ke jagoranta suke kai hare-hare akan ‘yan tawayen Houthi da ke kokarin mamaye manyan garuruwan kasar.
Ya zuwa yanzu wannan yaki ya, ya saka dubban mutane cikin halin kakanikayi.
A baya, sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, ya tattauna da masu fada a ji a bangaren ‘yan Houthi, inda ya yi kira ga ‘yan tawayen da su amince da shirin tsagaita wutar.
Ana tunanin ‘yan tawayen wadanda mabiya akidar Shi’a ne, kuma suke goyon bayan Mr Saleh, suna samun taimako ne daga kasar Iran.