Jamian bada agaji na Majalisar Dinkin Duniya sun roki kasar Saudiya da ta daina kai hari ga tashan jirgin saman Yemen, domin yin hakan ya lalata hanyoyin sauka da tashin jiragen sama na kasar. Yanzusun zamo yanzu basu da anfani.
Babban jamiin bada agajin Mr Johnane Van der Klaauw yace yanzu haka isa tashan jirgin yayi wuya sabooda rashin kyawon hanya, abinda ya kawo cikas ga kai kayayyakin agaji, ko kuma kaiwa ga jamian dake aiki wurin, haka kuma kai magunguna da wasu muhimmam abubuwan bukatu tare da kwashe wadanda suka yi rauni domin a yi musu.
Yace yanzu wurin da ya rage kawai shine babban filin jirgin saman Sanaa sai kuma tashar jirgin ruwa.
Ma’aikatan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya dake aiki a Yemendin sun ce rashin man feturya tilasta su dakatar da rarraba abinci a wasu yankuna, haka kuma sunce harin saman da Saudiya kewa jagoranci na cikin abinda ya taka wa aikin nasu birki.
Majalisar Dinkin Duniya tace sama da mutane dubu 1 da dari 2 ne aka kashe yayin da wasu dubu dari 3 suka yi kaura suka bar muhallinsu a cikin watanni biyu da suka gabata.
Kasar Saudiyya dai tana kokarin ganin ta fatattaki yan tawayen Houthi ne domin dawo da shugaba Abdu Rabu Mansour Hadi da duniya ta sani kuma ta amince dashi a matsayin shugaban kasar ta Yemen.