Hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa a yau akwai ‘yan gdun hijra sama da miliyan 65 a duk fadin duniya kuma kashi 10 ciki sun arce daga gidajensu ne a bara.
Hukumar ta kara da cewa rabin wannan adadin ‘yan gudun hijra kananan yara ne.
Shugaban hukumar Fillippo Grandi ya ce wannan sako ne ga kasashen duniya masu arziki da ke nuna cewa “idan ba a magance wata matsala ba, za ta iya zuwa ta sami mutum har inda ya ke.”
A Najeriya miliyoyin muta ne suka fice daga muhallansu sanadiyar rikicin Boko Haram a arewa maso gabashin kasar, kana a jamhuriyar Nijar da Kamaru ma dubban mutane sun fice daga gidajensu.
Wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdulaziz da ke Yola, ya leka wani sasanin ‘yan gudun hijra da ke jihar Adamawa kamar yadda za ku ji:
Your browser doesn’t support HTML5