Al’ummomin kauyen Tattara da sauran kauyukan da rikici ya daidaita a karamar hukumar Kokona a jihar Nasarawa sun bukaci gwamnati ta samar da tsaro don su koma yankunansu su yi noma.
Kusan makonni uku kenan tun bayan da wani rikici tsakanin manoma da makiyaya ya yi sanadin rasa rayuka da kone-konen gidaje, yayin da mutanen kauyukan da ke kewaye da garin na Tattara suka yi gudun hijira zuwa garin Garaku, shalkwatar karamar hukumar Kokona a Jahar Nasarawa.
Wani mai suna Musa Bala ya ce ya rasa ‘yan’uwansa an kuma kone gidaje da dama amma jama’a na zaune ne cikin tsoro da fargaba, dalilin da ya sanya kenan ba su koma kauyukansu ba, ga shi kuma damina ta kankama za su fara aikin gona.
Ardo Aliyu na karamar hukumar Kokona ya ce sun yi zaman sasantawa kuma da yardar Allah ba za a sake samun rikici a yankin ba.
Kwamishinan yada labarai da al’adu da yawon shakatawa na Jahar Nasarawa, Yakubu Muhammad Lawal ya ce gwamnati ta nada kwamiti da zai rika sasanta tsakanin wadanda ke zaman doya da manja don samun zaman lafiya mai dorewa a Jahar.
Duk da kokari da gwamnati ke cewa tana yi wajen magance rashin tsaro dai, yankuna da dama a jihohi na fuskantar nau’u’ka daban-daban na tsaro dake bukatar agajin gaggawa da magancewa.
A saurari cikakken rahoton Zainab Babaji:
Your browser doesn’t support HTML5