Wannan ya biyo bayan zanga zangar da ‘yan gudun hijrar suka yi a birnin Maiduguri cikin kwanaki biyun nan, kama daga ranar laraba zuwa ranar alhamis, lamarin da ya kaiga datse wasu hanyoyi, sai dai matakin da suka dauka bai zafafa kamar na ranar alhamis ba, inda daruruwan ‘yan gudun hijirar suka fito kan tituna suna kokawa akan rashin wadataccen abinci da ruwan sha a sansanoni.
Mataimakin gwamnan jihar Hon, Usman Durkwa, ya ziyarci wadannan ‘yan gudun hijira a lokacin da suke gudanar da zanga zangar, inda ya basu baki kuma daga bisani yayiwa manema labarai jawabi akan matakan da suka dauka.
Mataimakin gwamnan ya kara da cewa da yayi Magana da ‘yan gudun hijirar, sun bayyana masa cewa basu da wadataccen abinci, babu ruwan sha kum wasu daga cikin shuwagabannin su basa yi masu adalci, dan haka a matsayinsa na mataiamakin gwamna, alhakin ya rataya a wuyansa tunda gwamnan bashi nan, dan haka ya rushe kwamitin.
An gudanar da zanga zangar cikin lumana, kuma jami’an ‘yan sanda sun ba jama’ar kariya.
Domin Karin bayani saurari rahoton Haruna Dauda Biu.
Your browser doesn’t support HTML5