Shugaban Bankin Dr Ali Madani wanda yake ziyara a Najeriya ya gana da shugaban Najeriya wanda ya yabawa bankin saboda irin goyon bayan da yake ba kasar a harkokin cigaba.
Shugaba Buhari ya yi la'akari da irin taimakon kudi da bankin ya bayar wurin gina wasu ababen moriyar jama'a a jihohin Osun da Kaduna da Jigawa da Neja da Katsina da Kano da Ebonyi, lamarin da Shugaba Buhari yace shaida ce ta kaunar bankin wurin inganta ayyukan taimako.
Buhari yace "godiyarmu ta kasa bisa ga yadda ka daga bankin ya kai inda yake yau cikin shekaru arba'in da daya. Yanzu da zaka yi ritaya mun gode maka da irin shugabanci nagari da kayi wanda duk duniya ma tn amince da hakan" inji Shugaba Buhari.
Buhari ya kuma godewa bankin da sauran rassanta dangane da irin gudummawar da suka ba 'yan gudun hijiran da rikicin Boko Haram ya daidaita a arewa maso gabashin Najeriya.
Shugaba Buhari ya tabbatarwa shugaban bankin cewa, Najeriya, wadda tana cikin kasashen da suke da dimbin jari a bankin, zata cigaba da yin iyakacin kokarinta ta cika duk alkawuran dake kanta da suka jibanci bankin tare da sauke nata nauyin..
Yayinda yake maida martani Dr. Madani ya yabawa Shugaba Buhari akan sakamako mai kyau da yake samu sanadiyar yaki da cin hanci da rashawa.
Yace ashirye bankin yake ya samo kudade daga kasashen Larabawa da zasu taimakawa gwamnatin Najeriya da kamfanoni masu zaman kansu wajen aiwatar da ayyukan cigaba musamman a fannin noma da aiwatar da ayyukan cigaba.