Kungiyar masu motocin sufuri a Najeriya ta gudanar da babban taron ta na kasa a Mina, fadar gwamnatin jihar Neja, kungiyar ta ce ta shirya taronne domin duba manyan matsalolin da suka hana harkokin sufuri sukuni a kasar.
Daga cikin manyan matsalolin harda batun rashin kyawon hanyoyin mota a fadin kasar, lamarin da ke haddasa tafka asarar dinbin rayukan jama’a tare da dukiya ta miliyoyin kudi, kamar yadda shugaban kungiyar na Najeriya Alhaji Kasim Ibrahim Batayya ya bayyana.
Shugaban ya kara da cewa ko cututtuka irin su kanjamau, da zazzabin cizon sauro da sauran su basa haddasa rasa rayukan jama’a kamar hadarin mota a Najeriya.
Ko baya ga rashin kyawon hanyar motoci akwai matsalar barayi dake addabar masu motocin sufurin a cewar babban sakataren kungiyar Mr Aloga Ogbogo, ya yi Karin hasken cewa lokuta da dama ‘yan fashi kan tare manyan motocin saboda rashin kyan hanyoyi su yi masu fashi, wasu lokuta ma har sukan hallaka direbobin.
A yanzu dai fatar masu motocin sufurin na Najeriya shine a rage masu yawan kudaden harajin da ake karba daga hannunsu a kusan kowace karamar hukuma ta Najeriya. Alhaji Muhammad Umar Barden Patiskum shine shugaban masu motocin sufurin na jihar Yobe, ya ce baya ga kudaden da suke biya na kamfani, ana takura masu biyan wasu kudaden daban.
Masana harkokin tattalin arziki sun bayyana cewa inganta sha’anin sufuri na daya daga cikin hanyoyin bunkasa tattalin arzikin kasa.
Domin Karin bayani ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.