Daruruwan ‘yan gudun hijira da hare-haren ‘yan Boko Haram ya shafa ne suka gudanar da zanga zangar lumana a Yola fadar jihar Adamawa, kan batun kudaden dauki da bankin duniya wato World Bank da hadin gwiwar gwamnatin Najeriya su ka ba da domina tallafa masu.
An ba da kudaden ne a karkashin shirin tallafawa da kuma samar da ayyukan yi ga matasa na Youth Employment and Social Support Operation wato YESSO.
Su dai ‘yan gudun hijirar da suka famtsama zuwa bankin FCMB, da ke da alhakin raba kudaden, sun nuna bacin ransu na yadda rijiya ta ba da ruwa amma guga na neman hanawa.
Sun ce, wasunsu sun soma samun kudaden to amma kuma kwatsam, sai bankin ya dakatar da ba da tallafin.
Ganin yadda lamarin ke neman kazancewa ne ya sa tsohon jami’in kula da shirin na YESSO a jihar Adamawa, Abdulhamid Muhammad Jika, garzayawa zuwa bankin amma da kyar ya sha a hannun fusatattun ‘yan gudun hijiran.
Sai dai duk kokarin ji daga bakin shi sabon shugaban shirin a jihar Adamawa, Mr Kwoji Kwaghe, abin ya cutura wanda kawo yanzu tuni aka tsaida ba da kudaden.
Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdulaziz daga Yola:
Your browser doesn’t support HTML5