A wani kokari da kwararru ke ganin hanya ce da Najeriya za ta kai ga ciyar da al'ummarta, Shugaba Mohammadu Buhari ya sa hannu a dokar da zata taimaka wajen habbaka noma a kasar, tare da ba manoma damar daukar wasu matakai da za su kawo ci gaba.
Babban Mai taimakawa Shugaban kasa a majalisar wakilan Najeriya honorabul Omar El-Yakub, ya yiwa Muryar Amurka karin haske akan abubuwan da dokar ta kunsa.
El-Yabub ya ce dokar za ta hukunta duk wani wanda yayi algus a harkar sayar da takin zamani ko hanyar sarrafa shi; kamar kokarin canza launinsa, ko sake ma shi suna, ko ma sauya ma shi mazubi. Dokar ta ce za a iya hukunta mutum idan an kama shi da laifi sannan za a iya cin mutum tara daga naira miliyan biyar zuwa miliyan goma.
A wani abu mai kamar nuna jin dadin amincewa da wannan doka mataimakiyar shugabar Mata Manoma ta Kasa Hajiya Bilkisu Mohammed, ta ce manoma sun dade suna jiran wannan doka da za ta sa su ji dadin amfani da takin zamani saboda a sami abinci. Bilkisu ta ce kafin zuwan wannan doka, idan manomi ya sayi buhun taki wanda aka yi wa algus har yana zama abin tsoro saboda yadda ake surka shi da abubuwa daban-daban marasa amfani.
Shi kuwa mataimakin shugaban kungiyar Masu Masana'antu da Aikin Noma ta kasa (wato NACCIMA) Alhaji Sanusi Maijama'a Ajiya, ya ce matakin da Shugaban kasa ya dauka yayi daidai amma sai an fito da sharrudan da za a bi wajen aiwatar da dokar, domin wasu ba sa bin doka ko umurnin Shugaban kasa kai tsaye.
Dokar, ta inganta harkar noma ta hanyar samun ingantaccen taki ta na cikin dokoki 5 da majalisar kasa ta 8 da ta shude ta amince da su amma sai yanzu shugaba Mohammadu Buhari ya sa hannu bayan an yi ma ta gyara.
Ga karin bayani cikin Sauti.
Facebook Forum