‘Yan Gudun Hijira Sun Dawo Gamborum Ngala

Yan gudun hijira daga Kamaru

Rahotanni dake fitowa daga garin Gamborum Ngala dake jihar Borno na nuni da cewa, ‘yan gudun hijira dake jibge a garin Patakwal dake kasar Kamaru, na tattara inasu inasu na dawowa gida Najeriya, sakamakon fatattakar ‘yan Boko Hara da sojojin Najeriya suka yi a wannan yankin.

A shekarar da ta gabata ne dai sojojin Najariya a karkashin jagorancin laftanar janar Tukuru Buratai, suka fatatakin ‘ya’yan kungiyar nan da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne da suka yi kakagida a wannan yanki na Gambarum Ngalan.

Sai dai tun a wancan lokacin, mazauna garin na samun mafaka ne a Kasar Kamaru, wadda tuni kasar Kamaru ta baiwa Najeriya wa’adi, na kwashe wadannan ‘yan gudun jiharan daga kasar.

A cikin hirarsu da Sashen Hausa, wadansu ‘yan gudun hijiar da suka dawo gida, sun bayyana gamsuwa da samun dawowa bayan sun shafe sama da watanni goma sha bakwai suna gudun hijira a kasar Kamaru.

Ga rahoton da wakilin Sashen Hausa Haruna Dauda Bi’u ya aiko daga Maiduguri, jihar Borno.

Your browser doesn’t support HTML5

Yan gudun hijira sun koma Gamborum Ngala-4"05